Majalisar Wakilai za ta gudanar da bincike kan sallamar ma’aikata kusan 600 da Babban Bankin Nijeriya ya yi daga aiki.
Kudurin ya biyo bayan amincewa a karkashin kudirin kula da kuken jama’a da dan majalisa Jonathan Gbefwi daga jihar Nasarawa ya gabatar.
Gbefwi ya bayyana cewa, CBN a wani bangare na wani gagarumin garambawul na rage yawan ma’aikata wanda ya shafi ma’aikata kusan 600,
ciki har da daraktoci da kusan dukkan ma’aikatan da ke ofishin Gwamnoni.
Ya ce, wannan garambawul, ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatan da abin ya shafa da kungiyoyin kwadago.














































