Home Labaru Korafin Zabe: Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da...

Korafin Zabe: Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Karar C4C

347
0

Kotun da ke sauraren karar zaben shugaban kasa, ta yi watsi da karar da gamayyar jam’iyyu na C4C ta shigar tana kalubalantar nasarar da shugaba Buhari ya yi a zaben shekara ta 2019.

Lauyoyin da ke kare shugaba Buhari da jam’iyyar APC Wale Olanipekun da Lateef Fagbemi, sun bayyana wa kotu cewa ba su ga takardar janye karar da C4C su ka ce sun mika wa kotu ba, lamarin da ya sa su ka nemi kotu ta yi watsi da wannan kara.

Sai dai kafin kotu ta jefar da wannan kara, lauyan wadanda su ka shigar da kara ya bayyana cewa, a ranar Litinin din nan ne su ka mika takardar janye karar, sai da ba su samu damar iya samun ta kai ga lauyoyin wadanda su ke kara ba. Daya daga cikin Alkalan kotun biyar Mai shari’a Mohammed Garba ne ya yi watsi da wannan kara.