Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya jaddada cewa akwai wani tuggu da masu hana ruwa gudu a fadar shugaban kasa suke kitsawa domin a samu matsala a zaben 2023, da zai kai ga a nada gwamnatin wucin gadi.
A wata hira da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES, gwaman El-Rufai, ya ce wadannan mutane dake zagaye da shugaba Buhari sun kasa sun tsare lallai dole fa yadda suke so haka Buhari zai yi, bayan ba su nufin Najeriya da Alkhairi.
Nasuru El-Rufai, ya ce shi ba mutum bane da zai ja bakin shi yayi shiru idan ya ga irin wadannan abubuwa na faruwa, dole ya fito ya fallasa komai cikin gaskiya komai dacin ta.
Gwamnan ya ce kowa ya sani akwai wasu gaggan makusantan shugaba Buhari da suka nemi kodai Ahmed Lawan, shugaban Majalisar dattawa ya zama dan takarar shugaban kasa a APC ko kuma Godwin Emefiele ya zama, kuma dukkan su sun wasa wukaken su dole sai daya daga cikin wadannan mutane biyu, sai dai hakar su bata cimma ruwa ba.
El-rufa’i, ya ce tun daga wannan lokaci wadannan mutane suka rika kitsa tuggu da makirci da sharri da bala’in dole sai an tarwatsa komai kowa ya rasa, to amma sunma ba za su bar su ba.
You must log in to post a comment.