Home Labarai Kishin Kasa: Sarkin Musulmi Ya Ja Hankalin Jami’An Sojin Najeriya

Kishin Kasa: Sarkin Musulmi Ya Ja Hankalin Jami’An Sojin Najeriya

135
0
images 6 4
images 6 4

Mai alfarma Sarkin Musulmi, ya yi kira ga sojojin Nijeriya kada su bari ƙabilanci ya shiga cikin al’amuran su,

yana mai cewa hakan na iya raba kan sojoji da ƙasa baki ɗaya.

Sarkin Musulmin ya yi wannan roƙo ne a lokacin ƙaddamar da sabon ginin shelkwatar rundunar sojojin Najeriya da ke Bauchi.

ya ce, a aikin soja babu wane Musulmi ne  wane Kirista ne, ko wane Bahaushene wane Igbo ne ko kuma wane Bayerabe ne,

domin ba’a taɓa sanin waɗannan abubuwa a shekaru da dama da suka gabata ba.

Mai alfarma sarkin Musulmi ya kuma gargaɗi ‘yan Najeriya su daina yi wa jami’an soji mummunan zato wajen gudanar da ayyuka daban-daban.

Leave a Reply