Tsohon mataimakain shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 da ya gabata Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar LP a 2023 Peter Obi na shirin haɗewa domin kawar da gwamnatin Apc.
Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe ne ya tabbatar da wannan yunkuri a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels,
inda ya ce dukkanin mutum biyu sun ɗauki darasi kan kura-kuran da suka tafka a baya, Suna kuma shirin haɗewa domin kayar da jam’iyyar APC a 2027.
Atiku da Obi sun samu ƙuri’u sama da miliya shida-shida a zaben da Bola Tinubu ya samu nasara da ƙuri’a sama da miliyan 8 a 2023.
Wannan ne ya sa masu sharhi ke ganin cewar ƴan takarar biyu sun lalata damar da suke da ita ta samun nasara a zaben da ya gabata.
A baya dai Atiku Abubakar da Peter Obi dukkaninsu mambobin jamiyyar PDP ne kafin daga baya suka raba jamiyyar siyasa kuma kowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Ibe ya ce ƴan Najeriya basu cancanci zama a yanayin da suke ciki ba a wannan lokaci, kuma ana cikin mummunan yanayi a ƙasar da ba’a taba ganin iirinshi, jama’a kuma basu da ƙwarin gwiwa.














































