Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya ce yanzu haka ‘yan kwangilar da su ka gina tituna da gadoji su na bin Gwamnatin tarayya bashin Naira biliyan 765 da Miliyan 100.
Fashola, ya ce an yi ayyukan ne a manyan titunan gwamnatin tarayya da manyan gadojin da ke kan titunan.
Ya ce an bada naira biliyan 110 da rabi wajen ayyukan manyan tituna, domin a fara biyan ɗimbin bashin da ya Gwamantin Tarayya a cikin kasafin 2022.
Fashola ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke kare kasafin shekara ta 2023 a gaban Kwamitin kula da ayyuka na Majalisar Wakilai.
Ministan, ya koka da yadda Nijeriya ke kasa ɗaukar nauyin gudanar da ayyuka ba tare da ciwo bashi ba, sannan ya yi ƙorafi dangane da yadda ba a danƙara wa Ma’aikatar Ayyuka maƙudan kuɗaɗe a kasafin kuɗi.