Home Labaru Kasuwanci Karya Doka: Babban Bankin Najeriya Ya Yi Gargadi Kan Sayar Da Naira...

Karya Doka: Babban Bankin Najeriya Ya Yi Gargadi Kan Sayar Da Naira Da Liki A Biki

163
0
Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar, ya zargi Babban Bankin Nijeriya da boye sabbin takardun Naira, lamarin da ya ce ya sa al’ummar jihar ke kwana bin layi domin cirar kudi a na’urar ATM.

Babban Bankin Najeriya CBN  ya jaddada gargaɗinsa ga jama’a a kan yin liƙi da takardar kuɗi ta Naira a lokacin biki.

A sanarwar da hukumar bankin ta fitar ta Twitter ta ce, saɓa wa dokar bankin ta 2007 laifi ne da zai sa a ci tarar mutum naira dubu 50 ko kuma ɗaurin gidan yari da bai wuce wata shida ba ko kuma duka biyu.

Laifukan da bankin ya zayyana ana yi da takardar kuɗin sun haɗa da, liƙi da sayarwa da cukuikuyewa da rubutu ko zane ko tattaka su ko rawa a kan su da dai sauran su.

Babban Bankin na Najeriya CBN ya fitar da wannan gargaɗi ne a daidai lokacin da takardar kuɗin ke ƙaranci sakamakon canjin takardar naira ta 200 da 500 da kuma 1,000 da bankin ya yi.

Leave a Reply