Home Home Karewar Kwantiragi: Benzema Zai Bar Real Madrid Bayan Shekara 14

Karewar Kwantiragi: Benzema Zai Bar Real Madrid Bayan Shekara 14

80
0

Fitaccen ɗan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Karim Benzema zai bar ƙungiyar bayan shafe shekara 14 a Santiago Bernabéu.

Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar da ta wuce, ya fara taka leda ne a Madrid a shekarar 2009 bayan ƙungiyar ta ɗauko shi daga Lyon.

Benzema mai shekara 35 zai bar Real Madrid ne bayan kwantiragin sa da ƙungiyar ya zo ƙarshe a kakar nan da muke ciki.

Benzema ya ci manyan kofuna 25 a tsawon shekaru 14 da ya yi a ƙungiyar, ciki har da kofunan Gasar Zakarun Turai na Champions Leagues biyar, tare da kofunan Laliga huɗu.

Ƙungiyar Real Madrid ta ce Benzema zaƙaƙurin ɗan wasa ne mai kyakkaywar mu’amala, kuma ya ɗaga martabar ƙungiyar dan haka yana da damar fayyace makomarsa.

Dan wasan ya buga wa Real Madrid wasa 647, ya kuma zura ƙwallaye 353, shi ne ɗan wasa na biyu da ya fi ci wa ƙungiyar ƙwallo bayan Cristiano Ronaldo.

Ana sa ran was an sa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne wanda Real Madrid ta kara da Athletic Bilbao a jiya Lahadi a wasan ƙarshe na gasar Laliga ta kakar bana.

Ana dai rade-radin cewar ɗan wasan zai koma taka-leda a ƙasar Saudiyya ne bayan da ya samu tayi mai gwaɓi daga wata ƙungiya a ƙasar.

Leave a Reply