EFCC ta bukaci a dage sauraron sabuwar shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello, inda tace har yanzu wa’adin kwana 30 na tsohon sammacin da aka bashi basu cika ba.
EFCC ta kuma bada belin mutanen da ake tuhuma tare da tsohon gwamnan Jihar Kogin, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu tare da bukatar kotun ta tsawaitawa Yahya Bello lokacin gurfana a gabanta.
A yayin zaman kotun gaban mai Shari’a Maryam Anenih ta babbar kotun tarayya ta birnin tarayya Abuja, lauyan EFCC Jamiu Agoro ya bayyana cewa har yanzu umarnin da kotun ta bayar a ranar 3 ga watan Oktoban da ya gabata bai daina aiki ba.
Ya kuma kara da cewa ranar da aka tsayar a baya ta 20 ga watan Nuwamba bata yi wa bangaren masu kara daidai ba.
Daga nan Mai Shari’a Anenih ta dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.














































