Home Labaru Kamfanoni Sun Yi Karin Kuɗin Ruwan Leda A Najeriya

Kamfanoni Sun Yi Karin Kuɗin Ruwan Leda A Najeriya

23
0

Kungiyar masu samar da ruwan sha a roba ko leda ta Nijeriya, sun sanar da anniyar su ta karin kudin ruwa daga naira 200 a kan jaka guda zuwa naira 300.

Wannan dai ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugabar kungiyar Clementina Ativie ta fitar a Abuja.

Ta ce karin kudin ya na da alaka da hauhawar farashi a fanin kayayyakin da su ke amfani da su da kuma yanayin tattalin arzikin Nijeriya.

Atibie, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su yi hakuri sakamakon yanayin da wannan karin zai iya jefa su.