Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC tare da hadin guiwar ma’aikatar man fetur ta OROTON sun ba ‘yan gudun hijira sama da dubu shida a jihar Adamawa tallafin kayayyaki na dimbin kudi.
Abubakar Yakubu, shugaban sashen lura da barna na kungiyar Red Cross a Najeriya, ya ba da kayayyakin ga ‘yan gudun hijirar da ke Malkohi a karamar hukumar Yola ta kudu a madadin kamfanonin.
Kayayyakin sun hada da kayan abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.
Yace akalla gidaje 1200 ne za su amfana da kayayyakin a tsakanin kananan hukumomi uku a jihar.
You must log in to post a comment.