Home Labarai Kama Yahaya Bello: EFCC Na Duba Yiwuwar Neman Taimakon Sojoji

Kama Yahaya Bello: EFCC Na Duba Yiwuwar Neman Taimakon Sojoji

48
0
YAHAYA BELLO and Ododo
YAHAYA BELLO and Ododo

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar yaƙi da cinhanci ta EFCC ta shigar kan tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Afrilu ne bayan lauyan EFCC, Kemi Phinro, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman ba saboda wani wanda yake da kariya na ba shi mafaka.

Lauyan ya ƙara da cewa hukumar na duba yiwuwar haɗa kai da dakarun soji don ganin sun kama tsohon gwamnan.

Tun a jiya Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Ododo ne ya fice da Yahaya Bello a motar sa lokacin da jami’an hukumar suka yi wa gidans a tsinke a Abuja.

EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2 a lokacin da yake gwamnan jihar ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Leave a Reply