Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya ce ’yan Najeriya suna rayuwar ƙarya kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, matakin da ya ce ya zama dole don hana ƙasar nan rushewa.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure inda ya samu wakilcin Mataimakin shugaban jami’ar Ilorin Farfesa Wahab Egbewole.
Ya ce Tallafin, wanda aka tsara don taimakon talakawa, ya zama yana cutar da su, inda ya kara da cewa rayuwar jin daɗin da ‘Yan Najeriya suka ɗauka ba gaskiya ba ce domin tana iya kai ƙasar nan ga rushewa.
Ya kara da cewa cire tallafin man fetur da karya darajar Naira matakai ne masu wuya, amma wajibi ne domin ceto makomar ’ya’yanmu.
A wajen taron, mataimakiyar shugaban tarayya ta Akure Farfesa Adenike Oladiji, ta bayyana cewa ɗalibai 6,405 ne suka kammala karatu, ciki har da 519 da suka samu sakamako mafi kyau.
Ta bayyana nasarorin da jami’ar ta samu a fannin koyarwa, bincike, da ci gaban al’umma.