Home Home Kada Ku Tausaya Min Don Na Faɗi Zaɓen Sanatan Zamfara – Sanata...

Kada Ku Tausaya Min Don Na Faɗi Zaɓen Sanatan Zamfara – Sanata Marafa

468
0

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Kabir Marafa, ya shaida wa magoya bayan cewa kada su tausaya ma shi don Aliyu Iƙira Bilbis na jam’iyyar PDP ya kada shi.

Bayan faɗuwar da Marafa ya yi a jam’iyyar APC, a zaɓen gwamna ma APC ta faɗi zabe a jihar Zamfara, inda Dauda Lawal ya kada tsohon Gwamnan jihar Bello Matawalle.

Sanata Marafa, ya ce abin tausayi shi ne wanda bai tashi ya taɓuka komai ba, amma rashin nasara tamkar taki ne ga shuka.

Marafa ya ce Tinubu zai saka ma waɗanda su ka yi wa jam’iyyar APC hidima da waɗanda su ka wahala saboda ita.

Kabir Marafa ya tabbatar da cewa, Shugaba Bola Tinubu zai cika alƙawarin da ya ɗauka na saka wa duk waɗanda su ka taimaka wa jam’iyyar APC kaiwa ga nasara da muƙaman da su ka dace da kowanen su.

LEAVE A REPLY