Jagoran adawa kuma dan takaran shugaban kasa a 2023 na PDP Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dokoki ta yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana wajen shirya taron jin ra’ayin jama’a kan sabon ƙudirin harajin ƙasa
A makon da ya gabata ne majalisar dattawa ta ƙasa ta yi wa ƙudirin karatu na biyu, inda kuma yanzu ta miƙa shi ga kwamitin kuɗi na majalisar domin shirya taron jin ra’ayin jama’a kan ƙudurin.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce kan ‘yan ƙasa ya haɗu wajen yin kira a samar da tsare-tsaren kuɗi bisa adalci da daidaito ga kowane yanki.
Ya kara da cewa matsayinsa na mai ruwa da tsaki, ya yi imanin cewa gaskiya da adalci da riƙon amana da kyakkyawan shugabanci, na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi.














































