Home Home Jirgin Saman Najeriya Ya Koma Jigilar Fasinjoji Kamar Yadda Bincike Ya Nuna

Jirgin Saman Najeriya Ya Koma Jigilar Fasinjoji Kamar Yadda Bincike Ya Nuna

88
0

Kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines, ya cire fenti da sunan Nijeriya daga jikin jirgin da aka nuna a matsayin na kamfanin jirgin saman Nijeriya.

Wata na’urar bin diddigi, ta ce yanzu haka kamfanin sufurin jiragen sama na Ethiopian ya na amfani da jirgin wajen gudanar da ayyukan sa.

An dai sake wa jirgin fenti da suna ne domin ya wakilci kamfanin jirgin saman Nijeriya, kamar yadda ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Hadi Sirika ya bukata.

Sai dai tuni an maida wa ainahin mamallakin jirgin wato Ethiopian Airlines kayan sa.

Bayanin jirgin daga wata na’urar bin diddigi ya nuna cewa, a jirgin ya taso daga Addis Ababa zuwa Mogadishu, daga bisani ya koma birnin Addis Ababa.

Wani dan jarida mai zaman kan sa David Hundeyin ya ja hankalin jama’a zuwa ga na’urar jirgin ta shafin sa na Twitter, ya na mai cewa an cire sabon sunan da aka sanya wa jirgin saman Nijeriya, sannan ya koma bakin aikin sa na jigila tsakanin Addis Ababa da Magadishu.

Leave a Reply