Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya aika da saƙonsa na jaje zuwa ga mazauna da masu shaguna da annobar gobara ta faɗa musu a kusa da tashar hukumar sufuri ta jihar da ke Minna.
Tashar Channels ta ruwaito gwamnan yana bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar, inda ya ce annoba ce gobarar, amma yana jajanta musu.
Ya kuma yi kira ga waɗanda lamarin ya shafa su karɓi ƙaddara, wanda a cewarsa hakan zai sa Allah ya mayar musu da alheri.
Ya ƙara da cewa yawaitar gobara, musamman a yankin Minna, abin tashin hankali ne, wanda hakan ya sa ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su wayar da kan al’umma, sannan ya ce gwamnatin domin rage musu raɗaɗi.