Gwamnan Jihar Kwara a Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq ya tsayar da gobe Juma’a 29 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu domin bayar da dama ga ma’aikatan jijhar su kammala rijistar zabe.
Gwamnan ya ayyana hakan ne saboda wa’adin da hukumar zaben kasar, INEC ta sanya na dakatar da aikin ranar 31 ga watan Yuli, a shirin da take na zaben 2023.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar ta Kwara musamman ma’aikata da su yi amfani da wannan dama ta hutun su yi rijistar domin zaben.
Kwara ta bi layin jihohin da dama na Najeriyar wajen bayar da hutu domin jama’a su je su yi rijistar zaben.