Tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC
na ƙasa Timi Frank, ya buƙaci shugaba Tinubu ya binciki
wasu masu manyan mukamai a tsohuwar gwamnatin
Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Timi Frank ya ce ya kamata Tinubu ya gudanar da bincike a kan zargin cin zarafin ofishin wasu daga cikin su, kuma kada a bari su guje wa hukunci.
Fimi Frank ya bayyana sunayen ‘yan majalisar ministocin Buhari da ya kamata su kasance a komar Hukumomin EFCC DSS.
Ya ce ya kamata a binciki Timipre Sylva, da Sanata Hadi Sirika da Abubakar Malami da Mele Kyari da Sadiya Umar Farouq da Hadiza Bala Usman Kanar Hammid Ali.
Sauran sun hada da – Babban jami’in Hukumar Kula da Tsaron Ruwa ta Nijeriya Bashir Jamo, da Tsofaffin manajojin daraktoci da shugabannin Hukumar Raya Yankin Neja-Delta NDDC da duk shugabannin tsaron da aka yi wa ritaya cikin kwanakin nan.














































