Jam’iyyar PDP ta gargadi Shugaba Tinubu a kan shiga yaki da jamhuriyar Nijar, sakamakon juyin mulkin da aka yi har aka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.
PDP ta ce kamata ya yi Tinubu ya watsar da irin wannan bakin tunanin, maimakon haka ya shiga tattaunawar diflomasiyya domin cimma nasarar da ake bukata.
Shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP Gwamna Bala Mohammed ya bayyana haka, bayan wani taron jiga-jigan jam’iyyar PDP da ya gudana a Abuja.
Gwamna Bala Mohammed, ya ce Gwamnonin PDP sun shawarci shugaban kasa da babban kwamanda da gwamnatin tarayya kada su shiga kowane irin yaki da Jamhuriyar Nijar, kan juyin mulkin da soji su ka yi a kasar baya-bayan nan, sai dai a yi amfani da duk wani salo na tattaunawar diflomasiyya.