Uwar jam’iyyar PDP ta kasa, ta sanarda yin azumin mako guda da addu’o’i domin samun nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kotun sauraren kararrakin zabe.
Wata majiya ta ce, za a fara addu’o’in ne daga ranar Alhamis 18 zuwa ranar Laraba 24 ga watan Mayu na shekara ta 2023.
Addu’o’in dai, za a gudanar da su ne a jam’iyyar da ke Wadata Plaza a birnin Abuja da misalin karfe 12 na kowace rana.
Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP dai sun shigar da kara a kotun suararen korafe-korafen zabe, a kan zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Hukumar Zabe mai Zaman Kan ta ta kasa.














































