Home Home Inuwa Yahya Ya Zama Sabon Shugaban Gwamnonin Arewacin Najeriya

Inuwa Yahya Ya Zama Sabon Shugaban Gwamnonin Arewacin Najeriya

93
0

Gwamnonin arewacin Nijeriya, sun zabi Gwamna Inuwa Yahya na Jihar Gombe a matsayin sabon shugaban su domin maye gurbin Simon Lalong na Jihar Filato.

Rahotanni sun ce, daukacin gwamnonin yankin arewa 19, sun amince da zabin Inuwa Yahaya ba tare da hamayya ba a wani taron da su ka gudanar a Abuja.

Yayin jawabi bayan tabbatar ma shi da mukamin, sabon shugaban gwamnonin ya sha alwashin gudanar da shugabanci nagari ba tare da nuna bambanci siyasa a tsakanin su ba.

Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce zai yi bakin kokarin shi wajen ganin ci-gaba da dorewar kungiyar, domin taimakawa wajen samar da yanayin ci-gaban al’ummar yankin da kuma sama masu makoma mai kyau.

Ya ce kamar yadda tsarin kungiyar ya tanada, zai dora daga inda shugabannin kungiyar da su ka wuce su ka tsaya, musamman abin da ya shafi bunkasa tattalin arziki da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply