Home Labaru INEC Ta Wallafa Dokokin Yin Kamfe Da Na Kashe Kuɗin Jam’iyyu

INEC Ta Wallafa Dokokin Yin Kamfe Da Na Kashe Kuɗin Jam’iyyu

29
0

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta amince da sakin dokokin da su ka shafi yaƙin neman zaɓe da yawan kuɗaɗen da ‘yan takara da jam’iyyu za su kashe a zaɓen shekara ta 2023.

Bayanin hakan ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da ilimatarwa a kan masu jefa ƙuri’a na hukumar Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Festus Okoye ya ce hukumar ta yi taro, inda ta tattauna a kan batutuwan da su ka haɗa da wallafa dokokin da su ka shafi gangamin yaƙin neman zaɓe, da tarurrukan siyasa da kuma kuɗaɗen da jam’iyyu da ‘yan takara ke kashewa.

Ya ce a yanzu an wallafa bayanai a shafin hukumar na yanar gizo, sannan za a raba wa jam’iyyu da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da kafafen yaɗa labarai kwafin bayanan.

Festus Okoye, ya kuma tunatar da jam’iyyun siyasa a kan nauyin da ke kan su na miƙa rahoto ga hukumar kamar yadda kundin dokar zaɓe ya tanada.