Home Labarai Inec Ta Sanar Da Ranar Sake Zaɓen Majalisar Jiha a Wasu Ƙananan...

Inec Ta Sanar Da Ranar Sake Zaɓen Majalisar Jiha a Wasu Ƙananan Hukumomi a Katsina

120
0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta kasa INEC reshen Jihar
Katsina, ta ayyana 14 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a
sake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Kankia da
Ƙanƙara da kuma Kurfi.

Hukumar ta ce zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa bai kammalu ba, don haka aka sake sa ranar da za a kammala su.

INEC ta ce dokokin ta ne su ka yi tanadin sake gudanar da zaɓe a rumfuna ko mazaɓun da aka samu hargitsi.

Za a dai gudanar da zaɓen ne a rumfuna shida daga mazaɓu biyar da ke Ƙaramar Hukumar Kankia, da rumfuna 17 a mazaɓu tara na Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara, da kuma rumfuna takwas a mazaɓu shida na Ƙaramar Hukumar Kurfi.

Leave a Reply