Home Labarai INEC Ta Ce Amfani Da Tsarin Yadawa Ta Intanet Na Nan Daram

INEC Ta Ce Amfani Da Tsarin Yadawa Ta Intanet Na Nan Daram

345
0

Hukumar zaɓe mai zaman kan ta a Najeriya INEC ta jaddada cewa ba ta da niyyar daina wallafa sakamakon zaɓukan da take gudanarwa a shafin ta na musamman na intanet da ta fara kai-tsaye.


Hukumar ta INEC ta ce tana wannan batu ne saboda abin da kira rashin fahimta daga wata hira da jami’an hukumar suka yi da wata jarida, tana mai cewa ba ta sauya matsayinta na bayyana sakamako kai-tsaye ba yayin da ake ƙirga ƙuri’a.


Wata sanarwar da Kwamashinan Ilimantarwa na INEC Festus Okoye ya fitar a ranar Lahadi ta ce domin samun tabbas, wallafa sakamakon ta intanet na nan kamar yadda aka gani a zaɓukan baya-bayan nan da aka gudanar a jihohin Ekiti da Osun.


Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani sauyi a zaɓuka masu zuwa, ciki har da babban zaɓen 2023, kuma tana tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa yaɗa sakamako ta intanet na nan daram, domin abu ne da ke ƙara wa zaɓuka inganci idan ‘yan ƙasa na bin sawun sakamakon rumfunan zaɓe ta shafi na musamman a ranar zaɓe.


Idan ba a manta ba, sashe na 60 da 62 da 64 na sabuwar dokar zaɓe ta 2022 ne suka ba INEC damar wallafa sakamakon zaɓuka a intanet saɓanin zaɓukan baya.

Leave a Reply