Home Labaru Iftila’i: Wutar Dajin El Dorado A California Ta Cinye Kadada Dubu 7...

Iftila’i: Wutar Dajin El Dorado A California Ta Cinye Kadada Dubu 7 A Kwana 2

474
0

Masu aikin kashe gobara fiye da 500 na ci gaba da kai dauki dajin El-Dorado da ke gabashin San-Bernardo na birnin California a Amurka don kashe gobarar da ke ci gaba da barna tun safiyar Asabar wadda zuwa yanzu ta kone kashi 5 cikin dari na dajin.

Tuni dai gwamnan jihar Gavin Newsom ya sanar da sanya dokar ta baci baya ga umartar ilahirin yankunan da ke gab da dajin na El Dorado su kauracewa matsugunansu a kokarin shawo kan wutar wadda ke ci gaba da barna.

Binciken sashen kashe gobara na Amurka ya sanar da cewa gobarar wadda zuwa yanzu ta cinye kadada fiye da dubu 7 ta samo asali ne daga sinadaran da aka yi amfani da su don sanya dumin dajin yayin wani shagulgulan murnar samun juna biyu da wasu ma’aurata suka gudanar cikin makon da ya gabata wanda ake kira ‘‘Gender Reveal Party’’.

Masu aikin kashe gobarar dai sun rika amfani da jiragen Shalkwafta wajen feso ruwa da sinadaran kashe gobara cikin dajin baya ga kwashe wasu da wutar ta sanya su a tsakiya tare da rufe musu hanya.

Sashen kashe gobarar da ke birnin na California, ya ce ko shakka babu za a hukunta wadanda aka gano su ne sanadin tashin gobarar wadda ke ci gaba da lashe dukiyoyi, yayinda za a tuhume su da lafin sakaci da kuma bijirewa doka.

Zuwa safiyar yau litinin dai yanayin zafi birnin na California yakai digiri 43 a ma’aunin Celcius.

Leave a Reply