Home Labaru Idan Ba Buhari Na So Ya Kawo Ruɗani Ba Ne Ya Janye...

Idan Ba Buhari Na So Ya Kawo Ruɗani Ba Ne Ya Janye Maganar Canja Sabbin Takardun Kuɗi -ACF

123
0
Kungiyar Dattawan Arewa, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele da kakkausar murya, su gaggauta janye maganar dakatar da kashe tsofaffin takardun naira da ya ke neman jefa kasar nan cikin ruɗani.

Gwamnan banki CBN da shi kansa shugaba Buhari sun bayyana cewa, lallai ba za a tsawaita ranar da gwamnati ta sa na daina amfani da tsofaffin rakardun kudin Najeriya ba.

Kungiyar Dattawan Arewa, ta gargaɗi gwamnatin tarayya cewa idan ta cigaba da cewa lallai ranar 31 ga watan Janairu ne za a dakatar da kashe tsofaffin takardun kuɗin, Nijeriya za ta afka cikin ruɗanin da ba ta taɓa shiga ba, domin talakawa ba samun kuɗaɗen su ke yi ba.

Ta ce babu sabbin kuɗi a bankunan da CBN ke cewa ya raba wa sabbin takardun kuɗin, kuma har yanzu tsofaffin kuɗi bankuna su ke badawa idan an je cire kuɗi.

Leave a Reply