Home Labaru Hukunta Tsoffin Shugabannin: Ana Zaben Jin Ra’ayoyin Jama’a Mexico

Hukunta Tsoffin Shugabannin: Ana Zaben Jin Ra’ayoyin Jama’a Mexico

49
0

A yau ‘yan kasar Mexico ke zaben raba-gardama, kan bukatar da shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador ya gabatar kan ko ya kamata a binciki tsoffin shugabannin kasar a kan laifukan da suka yi a zamanin mulkinsu.

Shugaban wanda ya ce shi ba zai kada kuria’a a zaben na rafaranda ba duk da shi ne ya bullo da bukatar, ya ce shugabannin na baya sun rika tafka ta’asa san ransu.

Sai dai masu sukarsa sun ce kuri’ar wani yunkuri ne na neman suna, da kuma neman kawar da hankalin jama’a daga shugaban da suke gani na neman zama dan kama-karya.

Ba shakka, tsarin shari’a na Mexico, yana matukar bukatar sauye-sauye na gaske a ra’ayin yawancin ‘yan kasar, domin a fagen siyasa ana tafiyar da abubuwa son rai, ba bincike, kusan ba a hukunta manyan masu iko ko jami’an gwamnati kuma cin-hanci da rashawa sun zama ruwan-dare.

Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador ya gabatar da wannan zabe na jin ra’ayin jama’a ne a matsayin wani mataki na gagarumin sauyin da yake son kawowa don yaki da rashawa, da kuma ganin an hukunta da dama daga cikin shugabannin kasar na baya kan laifukan da suka tafka.