Kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, sun bukaci bayar da hadin kai ga kotun hukunta maus aikata manyan laifuka ta duniya ICC, da ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
Ministan harkokin wajen Italiya, Antonio Tajani wanda ya bayyana hakan a taron kungiyar da ya gudana a kasar sa, ya ce akwai bukatar kasashe ‘yan G7 su bawa ICC hadin kai wajen aiwatar da wannan hukunci nata.
Tajani, wanda ya kasance cikin ministocin kasashen kungiyar da suka halarci taron, ya ce akwai bukatar G7 ta kasance mai magana guda,
Ba wai samun rarrabuwar kai kan abin da yake a bayyane ba.
Kasar Amurka wadda ta kasance guda daga cikin ‘yan kungiyar, ta yi watsi da matakin ICC, inda shugaba joe Biden ya bayyana matakin kotun a matsayin zalunci.
A makon jiya ne, kotun ICC ta fitar da sanarwar kama Netanyahu, da tsohon ministan tsaron sa Yoav Gallant da kuma jagoran Hamas, Ibrahim Al-Masri, bisa zargin su da aikata laifukan yaki a Gaza.