Home Labaru Hisbah Ta Kama Masoyan Da Su Ka Yi Aure Ba Tare Da...

Hisbah Ta Kama Masoyan Da Su Ka Yi Aure Ba Tare Da Izinin Iyayen Su Ba

610
0
Hisbah Ta Kama Masoyan Da Su Ka Yi Aure Ba Tare Da Izinin Iyayen Su Ba
Hisbah Ta Kama Masoyan Da Su Ka Yi Aure Ba Tare Da Izinin Iyayen Su Ba The implementation of Islamic Sharia Law across the twelve northern states of Nigeria, centres upon Kano, the largest Muslim Husa city, under the feudal, political and economic rule of the Emir of Kano. Islamic Sharia Law is enforced by official state apparatus including military and police, Islamic schools and education, plus various volunteer Militia groups supported financially and politically by the Emir and other business and political bodies. Fanatical Islamic Sharia religious traditions are enforced by the Hispah Sharia police. Deliquancy is controlled by the Vigilantes volunteer Militia. Activities such as Animist Pagan Voodoo ceremonies, playing music, drinking and gambling, normally outlawed under Sharia law exist as many parts of the rural and urban areas are controlled by local Mafia, ghetto gangs and rural hunters. The fight for control is never ending between the Emir, government forces, the Mafia and independent militias and gangs. This is fueled by rising petrol costs, and that 70% of the population live below the poverty line. Kano, Kano State, Northern Nigeria, Africa

Jami’an Hukumar Hisbah a jihar Kano, sun kama wasu masoya da su ka daura ma kan su aure ba tare da izini ko sahalewar iyayen su ba.

Masoyan biyu, wanda dukkan su mazaun unguwar Kurna ne a cikin garin Kano, sun dauki matakin auren junan su ne bayan sun yi ido biyu da wani mutum da matar sa su na rungumar juna a bainar jama’a yayin da su ke tafiya a kan hanya.

Daga nan ne masoyan su ka gayyaci abokan su domin su zama waliyyan su, inda su ka daura ma kan su aure a kan sadaki Naira dubu 20 kamar yadda mataimakin kwamandan Hisbah Shehu Tasi’u Ishaq ya bayyana.

Sai dai ya ce, da ya ke saurayin ba ya da kudi, Naira dubu biyu kacal ya ke da su a hannun sa, inda budurwar da aka sakaya sunan ta ta ranta ma shi cikon Naira dubu 18.

Shehu Ishaq ya kara da cewa, bayan watanni uku da auren sai matar ta samu ciki, amma ya ce ba za a kira zaman da masoyan biyu su ka yi da zaman zina ba, kuma abin da ke cikin matar ba dan shege ba ne.