Home Labaru Hazaka: Yamal Ya Lashe Ƙyautar Gwarzon Matashin Ɗan Ƙwallon 2024

Hazaka: Yamal Ya Lashe Ƙyautar Gwarzon Matashin Ɗan Ƙwallon 2024

325
0
Lamine Yamal 2024Golden Boy Award Okay ng 860x604
Lamine Yamal 2024Golden Boy Award Okay ng 860x604

Ɗan wasan tawagar Sifaniya da Barcelona, Lamine Yamal ya lashe ƙyautar gwarzon matashin ɗan ƙwallon 2024.

Jaridar Italiya, Tuttosport ce ke shirya bikin, wadda ke karrama fitatcen matashin ɗan wasan nahiyar Turai, mai shekara kasa da 17 da ya yi fice a taka leda a kakar tamaula.

Yamal, mai shekara 17 ya nuna kan sa a bara a Barcelona, wanda yake buga mata tamaula a koda yaushe, ya lashe Euro 2024 a Sifaniya a gasar Jamus a bana.

Ya ci ƙwallo ya kuma bayar da huɗu aka zura a raga, wanda aka ba ƙyautar gwarzon ɗan wasan gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Cikin wattan Oktoba, Yamal ya karɓi lambar yabo ta Kopa Trophy, mai daraja irin ta Ballon d’Or da aka yi bikin a bana.

Yamal ya ci ƙwallo shida ya bayar da takwas aka zura a raga a karawa 16 a dukkan fafatawa a kakar nan.

Ɗan wasan tawagar Ingila da Real Madrid, Jude Bellingham shi ne ya lashe kyautar gwarzon matashin ɗan wasa a 2023.

Leave a Reply