Home Home Harin Roka: Mutum Uku Sun Mutu a Siriya

Harin Roka: Mutum Uku Sun Mutu a Siriya

39
0

Akalla mutum uku ne suka mutu a arewa maso yammacin Siriya sakamakon harin wani makamin roka, a yankin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce an harbo makamin ne daga wani yanki da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan SDF.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari, wanda yayi sanadiyar mutuwar Wani ƙaramin yaro a birnin Azaz.

A ‘yan kwanakin baya-bayan nan an ga yadda Turkiyya ke zafafa kai hare-hare ta sama kan yankunan ƙurɗawa a Siriya da Iraƙi.

Matakin na zuwa ne bayan wani harin bam da aka kai birnin Santambul da ya halaka mutum shida tare da raunata sama da mutum 80.