Home Labaru Harin Matatun Mai: Amurka Za Ta Tura Sojoji Saudiyya

Harin Matatun Mai: Amurka Za Ta Tura Sojoji Saudiyya

208
0

Amurka ta bayyana aniyarta ta tura sojoji Saudiyya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar hare-hare ga matatu da kuma kamfanonin mai na kasar.

Sakataren tsaro na Amurka Mark Esper ya shaida wa manema labarai cewa sojojin da za a tura za su je ne domin tabbatar da tsaro, sai dai bai bayyana adadin dakarun da za a tura ba.

A makon da ya gabata ne dai ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka dauki alhakin kai hari ga wasu matatun mai biyu na Saudiyyar.

Sai dai Amurka da kuma Saudiyya sun dora alhakin kai harin ga Iran.

A ranar Juma’a ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sabbin takunkumai ga Iran inda kuma ya ce yana so ya guji yaki tsakanin kasashen.

Wannan sabon takunkumin da Mista Trump ya kakabawa Iran din zai fi mayar da hankali ne ga babban bankin Iran din da kuma kadarorinta.