Home Labarai Harin Cocin Ondo: Atiku Ya Bada Gudunmawar Miliyan N10 Ga Wadanda Abun...

Harin Cocin Ondo: Atiku Ya Bada Gudunmawar Miliyan N10 Ga Wadanda Abun Ya Ritsa Da Su

370
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bada gudunmawar naira miliyan 10 ga wadanda harin ta’addanci ya rutsa da su a cocin Katolika na Owo da ke jihar Ondo.

Yayin da ya kai ziyarar jaje ga masarautar Owo, Atiku ya yi Allah wadai da kisan masu ibadah da aka yi.

Atiku Abubakar dai ya samu wakilcin dan takarar kujerar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede da ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar.

Da ya ke jawabi a fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye, AtikuAbubakar ya yi korafi a kan halin da tsaron Nijeriya ke ciki a halin yanzu.

Basarake Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, ya yaba wa Atiku abubakar bisa gudummawar da ya bada.

Leave a Reply