Home Labarai Martani: Sarkin Musulmi Ya Ce Sarakunan Gargajiya Ba Su Tsoron Gwamnoni

Martani: Sarkin Musulmi Ya Ce Sarakunan Gargajiya Ba Su Tsoron Gwamnoni

298
0
Sa'adu Abubakar Sultan of Sokoto (1)
Sa'adu Abubakar Sultan of Sokoto (1)

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Mohammad Sa’ad Abubakar III ya musanta maganar da ake cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoni.

Mohammad Sa’ad Abubakar III Ya bayyana haka ne a wani taro na ƙungiyar ci gaban matasan arewa da Gidauniyar Tunawa da Sardauna ta shirya a Abuja.

Sarkin musulmin ya ce sarakunan gargajiya sun kasance jagorori a ƙasa tun kafin ta samu ƴancin kai, ya ƙara da cewa sarakunan sun fi gwamnonin fahimtar yanayin ƙasa.

Tun da farko dai, tsohon gwamnan jihar Neja ne, Babangida Aliyu, ya ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoni.

Amma da yake mayar da martani, sarkin Musulmi ya ce sarakuna ba tsoron gwamnoni suke yi ba suna girmama kan su ne, sannan suna girmamma gwamnonin domin suna da iko a jihohin su.

Ya ce duk lokacin da wani abu ya faru, suna mayar da shi zuwa ga Allah ne, sannan suna kawo sauyin kuma suna karɓar sauyi a yadda suka zo musu.

Leave a Reply