Home Labaru Haraji: Masu Motoci Za Su Rika Biyan Kudin Amfani Da Manyan Tittunan...

Haraji: Masu Motoci Za Su Rika Biyan Kudin Amfani Da Manyan Tittunan Najeriya

99
0
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje

Gwamnatin Tarayya ta amince da sake dawo da karbar haraji daga motoci a manyan titunan da ke fadin kasar nan.

Taron majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da sake dawo da Harajin da ake karɓa daga motoci a manyan tittuna da ke faɗin Najeriya.

Sai dai harajin ba zai shafi motocin gwamnati ko sojoji da ma’aikatu da bubura da kekuna ba.                                         

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya bada wannan tabbacin a nan Abuja, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin kara hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Ministan ya ce tun a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a 2003 aka kirkiro wannan haraji, amma aka watsar domin haka yanzu za a dawo da tsarin.

Daga karshe Fashola ya ce kananan motoci za su biya Naira 200, yayinda manyan motoci kuma zasu biya naira 500.