Home Labaru Hangen Nesa: Idan Na Fallasa Abin Da Ke Faruwa A Nijeriya Ba...

Hangen Nesa: Idan Na Fallasa Abin Da Ke Faruwa A Nijeriya Ba Bu Wanda Zai Iya Barci – TY Danjuma

441
0
TY Danjuma, Tsohon Ministan Tsaro
TY Danjuma, Tsohon Ministan Tsaro

Tsohon ministan tsaro Janar TY Danjuma, ya ce idan ya fallasa abubuwan da ke faruwa a kasar nan ‘yan Nijeriya ba za su iya barci ba.

Janar Danjuma ya bayyana haka ne, a wajen wani taron karrama wasu da lambar yabo tare da kaddamar da littafi a kan shekaru 70 da aikin jarida na kamfanin Tribune da ya gudana a jami’ar Ibadan ta jihar Oyo.

Ya ce a kasar Yarabawa kowa ya zama zabo kuma matsorata, sannan da alamun mutane ba su damu da abin da ke faruwa ba.

TY Danjuma ya cigaba da cewa, ana cikin halin dar-dar a Nijeriya, Kuma mutanen da su ka sanya jama’a cikin wannan halin sun cigaba a yau, don haka hanya daya ta neman tsira ya kamata a tashi tsaye.

Ya ce abubuwan da ‘yan jaridar bogi ke yi ba su taimakon al’umma, don haka akwai bukatar addu’ar Allah ya cigaba da yi wa kasar nan jagora, amma ‘yan Nijeriya kadai ne za su iya ceto kawunan su da kan su.