Home Labarai Hana Biza: Shugaba Buhari Ya Nemi Dubai Ta Dage Dokar Dake Kan...

Hana Biza: Shugaba Buhari Ya Nemi Dubai Ta Dage Dokar Dake Kan ‘Yan Najeria Biza

93
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE, wadda ta kai ga dakatar da ba ‘yan Najeriya takardar izinin shiga cikin ta, wato biza.

A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne hukumomin Daular larabawan suka dauki matakin dakatar da ba ‘yan Najeriya bizar, sai wadanda suke da fasgo na manya wato na diflomasiyya kawai.

Duk da cewa hukumomin ƙasar ta Larabawa ba su bayyana dalilin su na ɗaukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin ɗa’a da bin doka da oda da wasu ‘yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.

A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaran sa na Daular, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi ya yi maganar neman ɗage dakatarwar.

Leave a Reply