Home Labarai Hamas Ta Ce Adadin Mutanen Da Isra’Ila Ta Kashe A Gaza Ya...

Hamas Ta Ce Adadin Mutanen Da Isra’Ila Ta Kashe A Gaza Ya Zarce Dubu 40

50
0
264696
264696

Ma’aikatar lafiyar Gaza dake karkashin ikon kungiyar Hamas ta ce adadin mutanen da Isra’ila ta kashe tun bayan barkewar yakin da ta kaddamar wata 10 da suka gabata a yau ya zarce dubu 40.

Sanarwar tace adadin mutanen ya kai dubu 40 da 5, idan aka hada da wasu mutum 40 da ta kashe jiya, cikin su harda wata uwa da jariran ta ‘yan biyu da ta haifa.

Sanarwar ta kungiyar Hamas ta ce mutanen da suka jikkata sun kai dubu 92 da 401 sakamakon yakin da aka kwashe wata 10 ana tafkawa,

tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai wa Israila a ranar 7 ga watan Oktobar bara, hararen da suka hada da makarantu da asibitoci da sansanonin ‘yan gudun hijira.

A yau ne ake komawa tattaunawar zaman lafiyar da Amurka ke jagoranci tare da kasashen Masar da Qatar wanda kungiyar Hamas tace ba zata halarta kai tsaye ba.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a yau ya shaidawa taron majalisar dokokin kasar Turkiya na musamman cewar zai koma Gaza tare da sauran shugabannin kungiyar.

Leave a Reply