Home Labarai Hamɓarar Da Gwmanatin Assad: Al’ummar Syria Na Bikin Murna

Hamɓarar Da Gwmanatin Assad: Al’ummar Syria Na Bikin Murna

95
0
Syria+New+Flag+EDITED
Syria+New+Flag+EDITED

Dubun dubatar ƴan Syria sun yi dandazo a Damascas, babban birnin ƙasar da sauran birane domin bikin murnar hamɓarrar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad, ranar da suka kira ta ”farin ciki”.

An kunna waƙoƙin neman sauyin gwmanati a dandalin Umayyad da ke babban birnin ƙasar.

Taron na kama da wata gagarumar walima, inda iyalai suke riƙe ɗaga tutocin neman sauyi, yayain da mutane ke ci gaba da tururuwa lungu da saƙo na ƙasar.

A cikin wani bidiyo da ya fitar, shugaban ƴantawayen da suka hamɓarrar da gwamnatin ƙasar ya buƙaci al’umma su fita su nuna farin cikin su cikin kwanciyar hankali da lumana.

Leave a Reply