Home Labaru Halin ‘Yan Siyasa Na Ba Sarakuna Mamaki – Sarkin Zazzau

Halin ‘Yan Siyasa Na Ba Sarakuna Mamaki – Sarkin Zazzau

220
0

Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli
ya ce halin ‘yan siyasa ya na ba sarakuna mamaki.

Ya ce a lokacin da ‘yan siyasa ke yakin nema zabe su kan je wajen su, amma da zarar sun samu nasara ba a kara jin duriyar su sai bayan shekaru hudu.

Basaraken ya kara da cewa, sarakuna su na bukatar samun matsayi a kundin tsarin mulki ba wai saboda yukurin kirkiro wani bangare na gwamnati ba.

Sarkin Zazzau ya bayyana haka ne, lokacin da shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya ziyarce shi a fadar sa da ke Zariya ta Jihar Kaduna.

Ya ce ba za a iya taba kwatanta irin gudummuwar da sarakuna su ke badawa ba, domin su na taka muhimmiyar rawa tun farkon mulkin dimokuradiyya har zuwa yau.

Sarkin Zazzau ya cigaba da cewa, abin da ya ke ba su mamaki shi ne, mutane su na zuwa wajen su neman tabarraki lokacin yakin neman zabe, amma da zarar sun samu nasara ba za su sake dawowa ba sai lokacin zabe su kara tuntubar su.

Leave a Reply