Ga dukkan alamu lokacin da ‘yan Nijeriya da yawa za su samu zuwa aikin hajji ya kusa, bayan zababben Shugaban hukumar aikin hajji ta kasa Zhikrullahi Hassan ya yi alkawarin yanke kudin kujera idan majalisar dattawa ta tabbatar da nadin na sa.
Da ya ke jawabi a zauren majalisar dattawa a lokacin da ake tantance shi, Hassan ya ce kudin hajji yanzu ba abu ne da mutane ke iya biya ba, don haka akwai bukatar sake duba lamarin.
Ya ce irin wannan yunkurin ba zai bari al’ummar Nijeriya da ke burin sauke farali samun damar yin hakan ba, don haka ya ce zai kafa shirin tara kudin hajji da zai ba maniyyata damar tara kudi a hankali kafin lokacin hajjin.
Zhikrullahi Hassan ya kara da cewa, zai tabbatar da ganin an rage yawan kwanakin da ‘yan Nijeriya ke yi a kasar Sauddiyya yayin aikin hajji.
You must log in to post a comment.