Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta amfani da kwalekwale na haya domin sufuri a ruwan Bagwai zuwa Badau da ke Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar.
Umarnin na zuwa ne kwanaki bayan wani kwalekwale da ke dauke da fasinjoji kimanin 47, yawancinsu dalibai, ya yi hadari inda ya hallakka fiye da mutum 30.
Bayanin hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya fitar a makon day a gabata.
Sanarwar ta ce sakamakon daukar matakin, gwamnatin Jihar ta samar da motocin bas guda biyu domin jigilar mutane tsakanin garuruwan Bagwai da Badau.
Har ila yau Gwamnatin ta kuma sha Alwashin sayen sabbin kwalekwale guda biyu wadanda zasu rika zirga-zirga akan wannan kogi domin kaucewa yawan hadari da ake samu.
Bugu da kari Gwamnati jihar Kano ta yi Akawalin daukar tsauraran matakai domin kaucewa sake aukuwar makamancin wannan hadari anan gaba.
Daga karshe zata kaddamar da kwamitin bincike, wanda daga bisani zai mika shawarwarinsa ga gwamnatin jihar.
You must log in to post a comment.