Home Labaru Haɗarin Jirgin Sama: Mutum Takwas Sun Mutu A Milan

Haɗarin Jirgin Sama: Mutum Takwas Sun Mutu A Milan

25
0

Wani ƙaramin jirgi ya faɗa cikin wani gini a birnin Milan inda dukacin mutane takwas da ke cikin jirgin suka mutu.

Jirgin ya tashi ne daga filin jirgin sama na Milan Linate kuma ya nufi tsibirin Sardinia, amma ya faɗi ɗan lokaci kaɗan bayan da ya tashi a waje-wajen birnin.

Shaidu sun ce sun jiyo wata ƙara a lokacin da jirgin ya faɗa ginin mai hawa biyu sannan ya kama da wuta.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu yaro ne ƙarami a cewar kafofin yaɗa labarai na ƙasar.