Daju ta, ta ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin ganin Najeriya ta fara sarrafa magunguna a cikin gida nan ba da dadewa ba.
Daju ta bayyana haka ne a Abuja a yayin wani taron karramawa na masu sana’a da aka shirya mata,
biyo bayan karramawa ta duniya da kwalejin koyar da harhada magunguna ta Afirka ta Yamma ta yi mata.
Ta ce, ma’aikatar tana aiki tare da duk masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya don samar da ingantattun ayyuka,
da samar da kiwon lafiya ga duniya baki daya da kuma bude hanyoyin da za a tabbatar da samar da kayayyakin da kasa ke bukata a cikin gida.
Babban sakataren kwalejin koyar da magunguna ta Afirka ta Yamma, Farfesa Ibrahim Adekunle Oreagba,
ya ce, karramawar da aka yi wa Daju, yawanci ana ba mambobin kungiyar da suka kasance shugabanni a kasashen da suke ne.














































