Gwamnonin Jam’iyyar PDP na yankin Kudu maso kudancin Nijeriya, sun yanke hukuncin ganawa da kungiyar gwamnonin da su ka bijire wa matsayin jam’iyyar bayan zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa da Atiku Abubakar ya samu nasara.
Bayan wata ganawa da su ka yi a Jihar Bayelsa, Gwamnonin sun ce za su gana da kungiyar G-5 da ta dade ta na tauna tsakuwa dangane da zaben da kuma bukatar ganin shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerar sa.
Kungiyar G-5 daita kunshi Gwamna Wike na Rivers da Samuel Ortom na Benue da Ifeanyi Ugwanyi na jihar Enugu da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Seyi Makinde na jihar Oyo, wadanda su ka kekashe kasa cewa dole sai jam’iyyar ta biya masu bukata kafin yi wa Atiku yakin neman zabe.
Gwamnonin yankin kudu maso kudancin Nijeriya, sun ce za su shiga tsakani domin dinke barakar da aka samu, duba da cewa lokacin zabe ya na kara karatowa.
Gwamnan jihar Bayelsa da ya karbi bakuncin taron, ya jaddada goyon bayan su ga takarar Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa, wanda shi ma ya samu halartar taron.
You must log in to post a comment.