Home Labarai Gwamnoni Sun Kai Wa Shettima Ziyarar Ta’aziyya

Gwamnoni Sun Kai Wa Shettima Ziyarar Ta’aziyya

66
0
Kashim Shettima 1
Kashim Shettima 1

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), ya jagoranci takwarorin sa wajen ziyarar ta’aziyyar ga mataimakin shugaban ƙasa,

Kashim Shettima, kan rasa surikar sa bayan dawowar sa birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba.

Gwamnonin, sun yi addu’ar Allah ya jiƙan surukar mataimakin shugaban ƙasa, marigayiya Hajiya Maryam Albishir.

Da yake godiya da ziyarar, mataimakin shugaban ƙasa, ya nuna jin daɗin sa kan ta’aziyar da gwamnonin suka kawo da yadda suka nuna tausayi da goyon baya a gare shi.

Shettima ya yaba da haɗin kan Gwamnonin da Gwamnatin Tarayya ya kuma yi kira a ƙara ba da hadin kai dan goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.

Leave a Reply