Home Labaru Ilimi Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa Tetfund Miliyan Dubu 208

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Wa Tetfund Miliyan Dubu 208

457
0
Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ware wa hukumar kula da manyan makarantu ta Nijeriya ‘TETFUND’ kudi Naira miliyan dubu 208 domin kula tare da bunkasa manyan makarantun gwamnati da suka hada da jami’o’i, da kwalejojin kimiyya da fasaha, da na horar da malamai a fadin Najeriya.

Bayanin ya fito ne daga shugaban hukumar, Farfesa Suleiman Bogoro, a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki a sha’anin manyan makarantu da hukumar ta gudanar a a babban birnin tarayya Abuja.

Farfesa Bogoro, ya yi karin haske dangane da yadda aka kasa kudaden zuwa wadannan manyan makarantun, inda ya ce kowace jami’a da za ta ci gajiyar kudin, za ta samu Naira miliyan 826,  da dubu 684, da 392, yayin da kowani kwalejin kimiyya dafasaha an ware masa Naira miliyan 566,  da dubu 701, da 842, sai kwalejojin horar da malamai da kowanne zai samu Naira miliyan 542, da dubu 226, da 346.

Bugu da kari kuma, ya ce a karkashin tallafin karatu na musamman wanda manyan makarantu 18 za su ci gajiyar sa a shiyoyi shida da ke fadin Nijeriya, ya kunshi ware Naira miliyan dubu 3 ga jami’o’i shida, da Naira miliyan dubu daya ga kwalejojin kimiyya da fasaha da wasu Naira miliyan dubu daya da aka ware wa kwalejojin horar da malamai.

Leave a Reply