Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Kori ‘Yan Shirin N-Power 2,525

Gwamnatin Tarayya Ta Kori ‘Yan Shirin N-Power 2,525

384
0

Gwamnatin tarayya ta sallami mutane dubu 2 da 525 daga cikin wadanda su ka amfana da shirin N-Power a kan rashin zuwa wuraren da aka tura su aiki a fadin Nijeriya.

Wannan kuwa ya na zuwa ne, a daidai lokacin da wasu dubu 18 da 674 su ka ajiye aiki da kan su bayan samun aiki na dindindin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in sadarwa na shirin tallafi na kasa mai shari’a Bibiye, ya ce hukuncin ya biyo bayan rahotannin da su ka samu daga jihohi cewa wasu da su ka amfana da shirin sun dade ba su zuwa wuraren aikin su.

Ya ce shirin N-Power ba wajen rabon sadaka ne ba, don haka ya zama dole duk wanda aka dauka ya rika zuwa aiki domin ita ce manufar shirin.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta bullo da shirin N-Power ne a shekara ta 2016, a wani yunkuri na samar da ayyuka ga matasa ‘yan tsakanin shekaru 18 da 35 da su ka kammala karatu.