Gwamnatin tarayya ta bada sanarwar sake waiwayar harajin
shigo da kaya daga ketare a matsayin wani ɓangare na tsara
dokar harajin Gamayyar kasuwanci ta Afirka, lamarin da ya sa
ta yi ƙari a kan haraji ga jasashe masu shigo da shinkafa da
alkama da barasa da sauran hajoji guda 189.
Sabon ƙarin harajin na shekara ta 2023 dai ya ɗaga harajin shinkafar da ta haura kilo 5, inda za a biya harajin kashi 60 cikin 100 sabanin kashi 50 cikin 100 da ake biya a baya, sannan shigo da alkama ko fulawar cin-cin za a biya kashi 70 cikin 100, akasin kasha 50 cikin 100 da ake biya a baya.
Ministar kuɗi da kasafi Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana haka, inda ta ce wannan shi ne bada tabbacin tabbatar da sabuwar dokar ECOWAS ta shekara ta 2023, ta ƙarin haraji a kan kayan da aka shigo da su daga ketare zuwa cikin Afirka.
Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce an yi ƙarin harajin ne a kan shinkafa da alkama da taba sigari da barasa da sauran su.
Ministar ta ƙara da cewa, sabuwar dokar ƙarin harajin ta haɗa har da ƙasashen da su ke shigo da kaya a karon farko zuwa ƙasashen Afirka, kuma ana sa ran dokar ta fara aiki tun ranar 1 ga watan Mayu na shekara ta 2023.














































